'Yan sandan yankin sun ce akalla mayakan masu tada-kayar-bayan na kungiyar Maute su 20 ne suka kai hari kan gidan-mazan ranar Asabar din da ta gabata, inda suka kwace makaman da ke hannun gandirobobi.
A makon jiya ne aka kama masu tada-kayar-bayan, lokacin da aka same su da wasu rokoki kirar cikin gida, jibge a cikin wata mota.
Akalla Fursunoni 15 ne suka arce daga gidan-yarin, bayan mayakan kungiyar masu tsaurin-ra'ayin.
Mayakan kungiyar Maute dai sun yi kaurin suna wajen kai harin bam da sace mutane a yankin Mindanao, inda ake da musulmi 'yan kasa tsiraru.288